Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

  • Author: Vários
  • Narrator: Vários
  • Publisher: Podcast
  • Duration: 3:46:28
  • More information

Informações:

Synopsis

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Alumma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalinariziki, aladu da dai sauransu

Episodes

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda matsalar tsaro ke komawa ɗanya a Najeriya

    19/11/2025 Duration: 10min

    Da alama masu ɗauke da makamai a Najeriya sun koma gidan jiya na sace-sacen dalibai, garkuwa da mutane da ajalin waɗanda basu ji basu gani ba gadan-gadan, yayin da a cikin kwanaki huɗu kacal aka yi awon gaba da mutum 145. Wannan na zuwa ne a yayin da matsalolin tsaro ke sake ta’azzara a sassan arewacin ƙasar, ciki har da satar ɗaliban da aka yi a jihar Kebbi, sai kuma labarin da ake ta yamaɗiɗin cewa mayaƙan ISWAP sun yi garkuwa da wani janar din soji tare da kashe shi a arewa maso gabashin Najeriyar. Shin kun gamsu da yadda jami’an tsaro ke aiki a yankunan ku. Me kuke ganin ya kamata hukumomi su yi domin kawo ƙarshen zulumin da jama’a ke ciki? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu sauraro kan rashin samun tikitin zuwa gasar kofin duniya da Najeriya ta yi

    18/11/2025 Duration: 10min

    A ranar Lahadin da ta gabata Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ta kawo ƙarshen fatan Najeriya na samun tikitin halartar gasar cin kofin duniyar da za ayi a shekara mai zuwa. Karo na biyu kenan a jere da Najeriya ke rasa damar haska wa a gasar ta Tamula mafi daraja a Duniya. Waɗanne dalilai ne ke janyo wa Najeriya wannan koma baya a sha’anin ƙwalllon ƙafa? Wanene ya gaza sauke nauyin da rataya a wuyansa a tsakanin masu alhaki a wannan fage? Ta yaya kuma za a magance matsalar? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakin ku a kai. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

  • Ra'ayoyin masu saurare kan rangadin da Tchiani ke yi a jihohin Nijar

    17/11/2025 Duration: 10min

    Shugaban gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, ya ziyarci jihohi daban-daban na ƙasar, da nufin sanin halin da al’umma ke ciki da kuma sanar da su irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen magance matsalolinsu. Ya kuke kallon wannan ziyara ta Janar Tchiani? Kuna ganin ziyarar tazo a lokacin da ya kamata? Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Abida Shu'aibu Baraza...

page 2 from 2