Kasuwanci

Al'ummar Nijar sun rungumi tsarin hada hadar kuɗi ta manhajar waya

Informações:

Synopsis

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen ƙasar ta Nijar. Samun damar aika kuɗaɗe ta hanyar amfani da manhajojin wayar hannu ba tare da yankar kuɗin haraji masu dama ba, dai tuni ya kawo sauyi dangane da hada-hadar kuɗi a Jamhuriyar ta Nijar, lamarin da ya zo a daidai lokacin da aka takaita fitar da kuɗaɗe daga Bankuna bayan juyin Mulki, tsarin da ya sa mutane da dama masu asusun ajiya a bankuna rungumar mahajojin na zamani a matsayin sabbin wuraren adana kuɗaɗen nasu.  Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.........