Wasanni

Shiri na musamman a kan gasar Olympics

Informações:

Synopsis

A yayin da wakilan kasashen ke kintsawa don zuwa gasar wasannin motsa jiki na Olympic da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa, shirin 'Duniyar Wasanni', ya kawo tarihin gasar, inda ya yada zango a Najeriya, wadda tawagar kwallon kafarta ta 'Dream Team' ta kasance ta farko a nahiyaar Afrika da ta lashe kofin kwallon kafa a gasar Olympiic a shekarar1996.Shirin ya samu damar tattaaunawa da wasu 'yan wasa da jami'ai da aaka dama da su a lokacin.   TARIHIN GASAR WASANNI TA OLYMPICGasar motsa jiki ta Olympics an fara gudanar da ita ne a karni na 8 a kasar Girka, sai dai daga bisani aka dakatar da ita.Bayan dakatar da gasar na tsawon lokaci, a shekarar 1940, kwamitin shirya gasar Olympics na Duniya IOC ya zabi babban birnin kasar Finland Helsinki don gudanar da gasar, amma sai dai sanadiyar barkewar Yakin Duniya na 2 aka sake dakatar ita.Bayan kawo karshen yakin, a shekara ta 1946, IOC ya yanke shawarar sake farfado da harkar wasannin Olympics na zamani, inda aka fara gudanar da wasannin gasar